An kashe fararen hula 4 a Yaman

An kashe fararen hula 4 a Yaman

Fararen hula 4 sun rasa rayukansu sakamakon ruwan bama-bamai a jihar Hajja da ke Yaman.

Kungiyar Likitocin Komai da Ruwanka ta bayyana cewar an kai hari kan wani asibiti da suke ba wa taimako wanda ke kan iyakar Yaman da Saudiyya a jihar Hajja.

A harin an kashe mutane 4, inda wani yaro karami kuma da aka kawo asibitin ya jikkata.

Sanarwar da Houthi ta fitar kuma ta ce kawancen kasashen Larabawa da Saudiyya ke wa jagoranci sun kai hari a jihar Hajja inda suka kashe fararen hula 4 da suka hada da yaro karami daya.

Babu wata sanarwa da Kawancen Kasashen Larabawar suka fitar game da batun.

 

News Source:  www.trt.net.tr