An kashe fararen hula 7 a Afganistan

An kashe fararen hula 7 a Afganistan

Fararen hula 7 da suka hada da mata da yara kanana sun rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka kai a jihar Kunduz da ke Afganistan.

Bam din da aka harba ya fada kan gidan fararen hula a gundumar Taluka.

Ma'aikatar Tsaro ta Afganistan ta sanar da cewar a harin da 'yan tawayen Taliban suka kai fararen hula 7 da suka hada da mata da yara kanana, wasu fararen hula 6 sun jikkata.

Kungiyar Taliban ba ta ce komai ba game da labarin.

A gundumomin Imam Ship f Dest-i Archi da ke jihar Kunduz, ana samun arangama a-kai-a-kai tsakanin jami'an tsaron Afganista da 'yan Taliban.

News Source:   ()