An kashe ko illata yara kanana sama da dubu 26 a Afganistan

An kashe ko illata yara kanana sama da dubu 26 a Afganistan

A tsakanin shekarar 2005 da 2019 da aka dauka ana yaki a kasar Afganistan, an kashe ku illata jikkunan yara kanana sama da dubu 26.

A wajen Babban Taron da Kungiyar Kare Yara Kanana ta "Save The Children", Majalisar Dinkin Duniya da Kasar Finlan suka shirya game da Afganistan, an yi ga kasashe masu bayar da tallafi da su agazawa kasar Yaman.

Rahoton ya bayyana cewar, sakamakon yakin da ake yi a Afganistan, a tsakanin 2005 da 2019 an kashe ku illata jikkunan yara kanana dubu 26 da 25.

Rahoton ya kuma ce, Afganistan na jerin kasashen duniya 11 d rayuwar yara kanana ta ke cikin hatsari, kuma a duniya a kasar ne aka fi kashe yara kanana.

Shugaban "Save The Children" a Afganistan Chris Nyamandi ya shaida cewar "Ku yi tunanin a ce a kowacce rana yaranku za su iya mutuwa daga harin kunar bakin wake ko harin bam ta sama. Wani abun bakin ciki ne ga yara da iyaye da ke Afganistan."

News Source:   ()