An kashe mataimakin gwamnan Kabul a harin bam

An kashe mataimakin gwamnan Kabul a harin bam

Mataimakin gwamnan Kabul Babban Birnin Afganistan Mahbubullah Muhibbi ya rasa ransa sakamakon harin bam da aka kai masa.

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida Tarik Aryen ya shaidawa manema labarai cewa, wani bam da aka dasa a motar mataimakin gwamnan Kabul Mahbubullah Muhibbi ya fashe a yankin Macroreyan 4 da ke Kabul.

Aryen ya ce, Muhibbi da Sakatarensa sun mutu yayinda wasu masu tsaron lafiyarsa 2 suka jikkata sakamakon harin.

Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.

News Source:   ()