An sace mutum 17 a jihar Nasarawa dake Najeriya

A jihar Nasarawa dake kasar Najeriya an kaiwa wani Masallaci farmaki inda  wasu 'yan bindiga su ka yi gaba da mutane 17.

Kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka rawaito wasu 'yan bindiga sun kaiwa wani Masallaci dake yankin Gwargwada-Sabo a jihar Nasararwa inda suka yi gaba da masallata 17.

Wadanda suka sace mutane 17 daga cikin wani Masallaci da suka hada da mata uku sun nemi 'yan uwansu su kai naira miliyan daya.

Kawo yanzu dai gwamnati bata ce kamai ba akan lamarin.

 

News Source:   ()