An tsare fiye da mutum dubu daya sanadiyar zanga-zanga a Tunisiya

An tsare fiye da mutum dubu daya sanadiyar zanga-zanga a Tunisiya

Jami'an tsaro a Tunisiya sun tsare fiye da mutum dubu daya sanadiyar zanga-zangar tabarbarewar tattalin arziki da jin dadin al'umman kasar.

Mataimakin Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama (LTDH) a Tunisiya Besam Itrifi ya yi bayani ga manema labarai akan lamarin jin kadan bayan taron kungiyar a babban birnin kasar. 
Ya bayyana cewa jami'an tsaron kasar sun kame fiye da mutum dubu daya sanadiyar zanga-zangar wadanda mafi yawansu yara ├Żan kasa da shekara 18 ne .

Ilrifi ya bayyana cewa an yi kamen ba bisa kaida ba kuma wadanda aka kaman an murguna musu.

Sanadiyar tabarbarewar tattalin arziki ne ya haifar da zanga-zangar a Tunisiya inda masu zanga-zangar suka lalata ginukan gwamnati da kone ababen hawa. 

Korona dake ci gaba da addabar duniya ta kasance annobar da ta kada zuciyar tattalin arzikin Tunisiya kwarai da gaske. 

Kasar Tunisiya wacce ke dogaro akan harkokin yawon bude ido da kuma hadahadar kasuwar canji da suka tabu kwarai da gaske sanadiyar annobar Korona ta samu karin rashin aikin yi a tsakanin matasar kasar.

 

News Source:   ()