Ana yunkurin sace bayanan hukumomin dake bincike game da Corona

Ana yunkurin sace bayanan hukumomin dake bincike game da Corona

An yi ikirarin cewa wasu 'yan kasar China na kokarin yin kutse a shafukan yanar gizon kungiyoyin da ke gudanar da bincike game da sabuwar kwayar cutar Covid-19.

Hukumar Leken Asirin kasar Amurka ta FBI da kuma ma'aikatar tsaron cikin gida sun gargadi hukumomi da kungoyoyin dake gudanar da bincike akan allurar rigakafi, magani da kayan gwajin kwayar cutar corona da su dauki matakan kare bayanansu.

Masu yin kutsen kwamfutar da ake ikirarin cewa suna da alaka da gwamnatin China, su na neman karbe ikon shafukan yanar gizon kungiyoyin da ke ayyukan bincike game da corona. Sabili da haka an yi kira ga wadannan hukumomi musanman na kasar Amurka da su dauki kwararan matakan kare bayanansu.

 

News Source:  www.trt.net.tr