'Yan ta'addar YPG/ PKK sun bude wuta kan matasa a Qamishli

'Yan ta'addar YPG/ PKK sun bude wuta kan matasa a Qamishli

Akalla mutum daya ya ji rauni sakamakon kungiyar ta'adda ta aware ta YPG/PKK da ta bude wuta kan wasu gungun matasa da ke gujewa dokar tilasta musu shiga kungiyar a yankunan da ta mamaye a arewa maso gabashin Siriya.

A lardunan Deir ez-Zur da Hasakah, inda larabawa ke da yawa, YPG/PKK na tilasta wa mutane shiga kungiyar.

YPG/PKK ta kame matasa kusan 15 a tsakiyar gundumar Qamishli na Hasakah don tilasta musu shiga kungiyar.

An samu labarin cewa wasu daga cikin matasan da ke adawa da shiga kungiyar sun yi kokarin tserewa kuma a kalla matashi daya ya samu rauni sakamakon harbin da aka yi musu.

'Yan ta'addan, wadanda suka taba aiwatar da irin wannan aikin a da, sun kame daruruwan maza 'yan shekaru 18 zuwa sama a cikin 'yan watannin a tsakiyar garin Hasakah da kuma a gundumar Qamishli, a samamen da suka kai kan gidaje da wuraren bincike.

'Yan ta'addar na kai samari da aka kame zuwa wuraren horarwa a Hasakah, a arewa maso gabashin kasar.

 

 

News Source:   ()