'Yan Taliban sun kashe jami'an tsaro 3 a Afganistan

Jami'an tsaro 3 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin bam da 'yan ta'addar Taliban suka kai da wata mota kan sansanin sojin Afganistan.

Kakakin fadar gwamnan jihar helmand Umar Zuvak ya shaşda cewar 'yan ta'addar na Taliban sun kai hari da mota makara da bama-bamai kan sansanin sojin kasa da ke yankin Yahchal na gundumar Girishk din jihar.

Zuvak ya ce an kashe jami'an tsaro 3, yayinda aka jikkata wasu 6 sakamakon harin.

Taliban ta dauki alhakin kai harin inda ta ce ta kashe sama da sojoji 10.

News Source:  www.trt.net.tr