"Shekarar 2021 ta ma'aikatan lafiya ce"

"Shekarar 2021 ta ma'aikatan lafiya ce"

Ministan harkokin kiwon lafiyar kasar Turkiyya Dkt. Fahrettin Koca ya bayyana cewa ba zamu iya biyan kokarin da ma'aikatan lafiya suka yi muna ba.

Ministan Koca ya bayyana shekarar 2021 a matsayar shekarar ma'aikatan lafiya.

Kamar yadda ministan ya yada a shafinsa ta Twitter ya bayyana matukar godiya ga ma'aikatan lafiya wadanda suka yi aiki tukuru tun bayan bulluwar cutar annobar Korona kawo yanzu.

Ya kara da cewa "Ina mai mika godiya ga dukkanin ma'aikatan lafiya da iyalinsu wadanda suka yi aiki tukuru tun daga ranar da annobar Korona ta bulla har ila yau. Ba zamu iya biyan ma'aikatan lafiya ladar aikinsu, muna masu mika godiya a garesu, shekarar 2021 tasu ce"
 

News Source:   ()