Armeniya na cigaba da sabawa yarjejeniyar tsagaita wuta

Armeniya na cigaba da sabawa yarjejeniyar tsagaita wuta

Sojojin Armenia sun sabawa yarjejeniyar tsagaita wutar da aka ayyanar tsakanin kasarsu da Azabaijan akan Nagorno-Karabakh.

Ma'aikatar Tsaron Azabaijan ce ta sanar da cewa, Armeniya ta aiwatar da ayyukan tsokana ta hanyar sabawa yarjejeniyar tsagaita wuta a yankunan Azabaijan da aka kubutar daga mamayarta.

A cikin sanarwar, an bayyana cewa Sojojin Azabaijan sun mayar da martanin da ya kamata kuma a halin yanzu suna cigaba da mutunta yarjejeniyar tsagaita wutan.

Nasarorin da sojojin Azabaijan suka samu a kokarin kubutar da yankunan Nagorno-Karabakh daga mamaya a ranar 27 ga watan Satumba ya tilasta wa Armenia sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar 10 ga Nuwamba.

News Source:   ()