Armeniya ta sake kaiwa farar hular Azerbaijan hari

Armeniya ta sake kaiwa farar hular Azerbaijan hari

An sanar da cewa Armeniya ta sake kai wa farar hular Azerbaijan hari.

Dakarun Armeniya sun sake kaiwa farar hular yankin Ganja da Mingechevir dake Azerbaijan hari.

Da yawan farar hula  kasa ta taushe su a ginar da ta rushe sakamakon kai harin.

Mataimakin shugaban kasar Azerbaijan Hikmet Hacıyev, ya bayyana cewa an samu hasarar rayukan farar hula.

Hikmet Hacıyev, ya yada a shafinsa ta Twitter da cewa,

"Armeniya wacce ke boyewa karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta na ci gaba da kai harin ta'addanci tare da aikata laifukan yaki. Ta sake kai hari a yankin Ganja da Mingechevir za'a bayyana hasarar rayukan da aka yi"

 

News Source:   ()