Babban Bankin Duniya za ta taimakawa ķasashe masu tasowa da allurar riga-kafin Korona

Babban Bankin Duniya za ta taimakawa ķasashe masu tasowa da allurar riga-kafin Korona

Babban Bankin Duniya ta ware dala biliyan 12 domin taimakawa ķasashe masu tasowa wajen magance da raba allurar riga kafin kwayar cutar Covid-19.

Kamar yadda babban bankin ta sanar da cewa tallafin zai kasance ne domin yiwa alumma biliyan daya allurar riga kafin kwayar cutar Covid-19. 

Sanarwar ta kara da cewa tallafin zai kasance ne ga ķasashe masu tasowa domin samawa alumman wadannan ķasashen tsaro da kuma kariya daga cutar Covid-19. 

Shugaban bankin David Malpass ya bayyana cewa wannan mataki ne da zai yakı cutar tare da kauda dukkanin matsalolin tattalin arziki da ya haifar.

 

 

 

News Source:   ()