Corona ta yi ajalin karin mutum 142 a Iran

Corona ta yi ajalin karin mutum 142 a Iran

A ranar juma’ar data gabata kasar Iran ta bayyana cewa kwayar cutar Corona ta kara yin ajalin wasu mutum 142 a kasar inda a jumlace mutum dubu 12, 447 ne cutar ta kashe a fadin kasar.

Haka kuma an kara samun mutum 2,262 dauke da cutar ta COVID-19, lamarin da ya kara yawan wadanda suka kamu da cutar a fadin kasar zuwa dubu 252,720, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar lafiyar kasar Sima Sadat Lari ta bayyana.

A jumlace mutum dubu 215,176 sun warke daga cutar a kasar an kuma sallamesu daga asibiti. Sai dai mutum 3,319 daga cikin masu fama da cutar corona a kasar na cikin mawuyacin hali.

A fadin duniya dai Corona ta yi ajalin mutum dubu 555,500 a kasashe 188 da wasu yankuna tun bayan bulluwarta a China a watan Disambar shekarar bara.

News Source:  www.trt.net.tr