Covid-19 ta kara bayyana a China

Covid-19 ta kara bayyana a China

Kasar China ta sake saka dokar hana fita waje a yankin Xinjinag mai zaman kansa wanda keda yankin Uighur da Musulmi suke bayan sake samun wasu mutum shida dauke da kwayar cutar corona.

Hukumar Lafiyar kasar ta bayyana cewa na samu wasu mutum 10 dauke da cutar wadanda tara daga cikinsu sun fito ne daga kasashen waje.

Wanda aka samu da cutar wanda ba daga kasar waje ya fito ba, dan yankin Urumgi ne dake karkashin babban birnin kasar.

Malaman lafiyan yankin sun bayyana cewa an samu wata mata mai shekaru 24 da corona an kuma kebe dukkanin ‘yan uwanta domin kula.
 

News Source:  www.trt.net.tr