Dakarun Isra'ila sun sake kai hari ta sama a Gaza

Dakarun Isra'ila sun sake kai hari ta sama a Gaza

Mutane 7 da suka hada da wani  Bayahude daya, sun ji rauni a yayin kalubalantar da aka yiwa matasan Falasdinawa a yankin tsohon garin Gabashin Kudus, wanda ke karkashin mamayar 'yan sandan Isra'ila.

‘Yan sandan Isra’ila sun sake katsalandan ga matasan Falasdinawan a Tsohon garin Gabashin Kudus, wanda ke karkashin mamayarsu.

Kungiyar Red Crescent ta Falasdinu ta sanar da cewa 'yan sandan Isra'ila sun raunata Falasdinawa 6 smamanen da suka kai, mutane 4 daga cikinsu an yi musu jinya a wurin da lamarin ya afku yayinda biyu daga cikinsu kuwa aka tilastu ga garzayawa dasu zuwa asibiti.

A cewar bayanan da aka samu daga shaidun gani da ido, an sanar da cewa wani Bayahude da ya zo wucewa ya ji rauni a kansa a katsalandan da ‘yan sandan Isra’ila suka yi wa Falasdinawa.

A gefe guda kuma, jiragen yakin mallakar sojojin Isra'ila sun kai wani hari ta sama a kan Gaza da aka yiwa kawanya.

Babu wanda ya rasa ransa ko ya ji rauni a cikin bama-baman da suka tashi a budddun wurare a sassa daban-daban na Gaza.

News Source:   ()