Dakarun kasar Turkiyya sun tarwatsa gungun 'yan ta'adda a Iraki

Dakarun kasar Turkiyya sun tarwatsa gungun 'yan ta'adda a Iraki

Dakarun sojin saman kasar Turkiyya da jirginsu kirar F-16 sun gano wani mabuyar 'yan ta'adda a yankin Avasin-Basyan dake arewacin Iraki tare da lalata shi nan take.

Ma'aikatar tsaron kasar Turkiyya ta sanar da cewa a yayin cigaba da yaki da ta'addanci jirgin rundunar sojin saman kasar lirar F-16 ya lalata wani mabuyar 'yan ta'adda a yankin Avasin-basyan dake arewacin Iraki.

Sanarwar ta kammala da cewa dakarun sararin samaniyya a koda yaushe suna kan aikinsu sun kuma kammala wani aikin nasu cikin nasara.

 

News Source:  www.trt.net.tr