Dalibai 561 sun kamu da Covid-19 a Koriya ta Kudu

Dalibai 561 sun kamu da Covid-19 a Koriya ta Kudu

An sanar da cewa akallan dalibai 561 sun kamu da kwayar cutar Covid-19 daga cikin mutum dubu 23, 952 dake dauke da cutar a Koriya ta Kudu.

A yayinda yake dangana bayanininsa daga bayanan da suka fito daga ma’aikatar ilimin kasar, jami’i, Jung Chan-min dan jam’iyyar adawar kasar ya bayyana cewa dalibai 561 daga makarantun firamaire zuwa sekandare daga watan Mayu zuwa 20 ga watan Satumba sun kamu da muguwar cutar.

Ya shaidawa kanfanin dillancin labaran Yonhap  da cewa a makarantar sakandare kusan dalibai 220 suka kamu. A babban birnin kasar Seoul ne dai aka fi samun yawan daliban da suka kamu da cutar.

An dai yi nasarar yiwa dalibai kusan 473 magani wadanda aka sallama inda kuma aka kebe wasu 88.

News Source:   ()