Fashewar tagwayen bama-bamai ya raunana mutum 5 a Siriya

Fashewar tagwayen bama-bamai ya raunana mutum 5 a Siriya

An sanar da cewa fashewar wani bama-bamai da aka ajiye a wasu wurare biyu a garin Bab dake kasar Siriya ya yi sanadiyar raunanan mutum biyar.

A garin Bab dake yankin da aka ci gaba da kauda ta'addanci bayan faramakin garkuwar Firat wasu bama-bamai biyu da aka ajiye sun tashi lokaci guda.

Lamarin ya yi sanadiyar raunanan mutum 5.

Ma'aikata kiwon lafiya sun garzaya da wadanda suka raunanan asibiti.

Haka kuma harin ya haifar da hasarar dukiyoyi.

A yayinda jami'an tsaro suka fara bincike akan lamarin ana ganin cewa kungiyar ta'addar YPG/PKK ne suka kai harin.

 

News Source:  www.trt.net.tr