Gobara a gidan kula da tsofaffi a Rasha

Gobara a gidan kula da tsofaffi a Rasha

Mutane 9 sun rasa rayukansu sakamakon gobarar da ta kama a wani gidan ajje tsofaffi a garin Krasnogorsk na kasar Rasha.

Sanarwar Bayar da Agajin Gaggawa ta Rasha ta ce gobarar ta kama a wani gidan kula da tsofaffi da ke garin Krasnogorsk da ke karkashin Babban Birnin Kasar Moscow.

An bayyana mutuwar mutane 9 inda aka kuma kama wasu 9 sakamakon lamarin.

An sanar da cewar akwai mutane 29 a cikin ginin lokacin da gobarar ta kama kuma an fara gudanar da bincike.

Rahotannin farko sun ce gobarar ta faro daga wajen ajje turiri kuma an shawo kan lamarin.

News Source:  www.trt.net.tr