Guguwar Zeta ta yi ajalin mutane 6 a Amurka

Guguwar Zeta ta yi ajalin mutane 6 a Amurka

Mutane 6 ne suka rasa rayukansu sakamakon guguwar Zeta da ta kunna kai kudu maso-gabashin Amurka.

Mahukunta sun ce guguwar Zeta ta kunna kai jihohin Louisiana, Georgia, Mississipi, North Carolina, Maruland da Virginia.

An bayyana mutuwar mutane 6 da suka hada da 1 a Louisiana, 1 a Mississipi da 4 a Alabama da Georgia.

A ranar Litinin 26 ga Oktoba guguwar Zeta ta taso daga Tsibirin Yucatan da Mekziko inda ta ke gudun kilomita 130 a awa daya.

A wannan shekarar guguwowin Laura da Delta sun illata jihar Louisiana.

 

News Source:   ()