Harin da ya kashe wani karamin yaro a Chicago

Harin da ya kashe wani karamin yaro a Chicago

An kashe wani yaro dan shekara 4 kuma wasu yara 7 sun jikkata a hare-haren da aka kai da makamai a birnin Chicago na kasar Amurka.

‘Yan sandan yankin sun sanar a wani taron manema labarai cewa yara 8 sun samu raunuka kuma daya daga cikinsu ya mutu, a hare-haren da aka kai a Chicago a karshen mako.

A cewar ABC News, an harbi Mychal Moultry mai shekaru 4 sau biyu a kai lokacin da harsasan da aka harba a gaban gidansa da ke gundumar Woodlawn na birnin suka shiga ta taga.

An kai Moultry asibiti amma ba a iya ceton sa ba.

Rundunar ‘yan sandan ta sanar da cewa za a ba da ladar dala dubu 9 ga duk wanda ya bayar da bayanai don gano wanda ya kashe Moultry.

An bayyana cewa sauran yaran 7 da suka jikkata sun haura shekaru 12.

News Source:   ()