Hukumar Yunus Emre na ci gaba da yiwa duniya hidima ta yanar gizo

Hukumar Yunus Emre na ci gaba da yiwa duniya hidima ta yanar gizo

Hukumar Yunus Emre Institute (YEE) wacce aka sani da yada al’adun Turkiyya a cibiyoyinta 58 dake fadin duniya ta ci gaba da ayyukanta ta yanar gizo ta gudanar da shirye-shirye daban-daban.

Hukumar YEE ta zabi ta ci gaba da ayyukanta ta yanar gizo ne sabili da kwayar cutar corona dake addabar duniya.

A hirar da shugaban YEE ferfesa Şeref Ateş ya yi da kanfanin dillancin labaran Anadolu ya bayyana cewar hukumar na farin cikin yadda take yada manyan alkaluman Turkiyya biyu  a fadin duniya watau al’adu da bunkasa.

A yayinda Ates ke bayyana muhimmancin al'adu ya kara da cewa idan har kasa bata samar da sabbin abubuwa bisa ga al’adarta ba, toh ko shakka babu zata manta da al’adun nata.

Ya kara da cewa al’ada abu ne da ya kamata a sani a sabili da haka muke kokarin yada al’adunmu ta yanar gizo kasancewar halin da ake ciki a hallin yanzu.

News Source:  www.trt.net.tr