Iran ta kyamaci zanen barkwancin da aka yi akan fiyayyen halitta a Faransa

Iran ta kyamaci zanen barkwancin da aka yi akan fiyayyen halitta a Faransa

Kasar lran ta kira wasu jami'an diflomasiyyar kasar Faransa dake ķasarta zuwa ma'aikatar harkokin wajen kasar akan nuna goyon bayan da wasu manyan jami'an gwamnatin Faransa da suka hada da Emmanuel Macron  ga zanen barkwancin da aka yi akan Annabi Muhammad (SAW) 

Kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen kasar lran ta sanar kasar lran ta yi matukar kyamar zanen barkwancin da aka yi akan Annabi Muhammad (SAW).

Sanarwar ta kara da cewa lran na matukar yin Allah wadai da irin ďabi'un shugabanin Faransa da wasu a Nahiyar Turai dake nuna batanci ga Musulmi. Sanar ta nanata cewa an kira shugaban diflomasiyyar Faransa a lran Florent Aydalot  inda aka sanar dashi cewa wannan ba abu ne wanda za'a taba amincewa dashi ba. 

 

News Source:   ()