Jirgin saman Indiya ya fado a yankin Kashmir

Jirgin saman Indiya ya fado a yankin Kashmir

An bayyana cewa, wani jirgin sama mai saukar ungulu mallakar Indiya ya fada wata madatsar ruwa da ke yankin Jammu Kashmir.

Jaridar Indian Times ta shaida cewa, jirgin saman samfurin 254 AA mallakar Indiya ya fada madatsar ruwa ta Basohli da ke Kathua.

An bayyana cewa, akwai a kalla mutane 5 a cikin jirgin.

Shugaban 'yan sandan Pathankot, Surendra Lamba ya shaida cewa, an aika da sojoji da ma'aikatan ceto zuwa yankin da hatsarin ya afku.

Ana kuma gudanar da bincike kan musabbabin hatarin.

 

News Source:   ()