Kanfanin jirgin saman Katar zai fara safara zuwa Istanbul

Kanfanin jirgin saman Katar zai fara safara zuwa Istanbul

Kanfanin jirgin saman kasa Katar ya bayyana fara safara zuwa birnin Istanbul sabili da fara sassauta matakan yaki da kwayar cutar Corona dake ci gaba da addabar duniya.

Kamar yadda kanfanin ya sanar a shafinsa na Twitter,

"Kanfanin jirgin saman Katar zai fara safara zuwa daya daga cikin manyan biranen da ya saba kai kawo watau Istanbul a ranar 13 ga watan Yuni.

Sanarwar ta kara da cewa kafin karshen watan Yuni kanfanin zai fara safara zuwa kasashe kusan 80 a fadin duniya.

 

News Source:  www.trt.net.tr