Karamin jirgin sama ya fado a Mekziko

Karamin jirgin sama ya fado a Mekziko

Mutane 6 sun rasa rayukansu sakamakon fadowar wani karamin jirgin sama a jihar Chihuahua da ke kasar Mekziko.

Labaran da jaridun kasar suka fitar na cewa jirgin samfurin TU206G ya tashi daga garin Camargo na gabashin kasar zuwa Sinaloa, inda ya fado a jihar Chihuahua.

Mahukunta sun bayyana cewar matukin jirgin leonilo Gonzalez Olivas da wasu karin mutane 5 sun rasa rayukansu a hatsarin.

An fara gudanar da musabbabin fadowar jirgin.

News Source:  www.trt.net.tr