Kaso 87.56 na marasa lafiya na warkewa daga Covid-19 a Indiya

Kaso 87.56 na marasa lafiya na warkewa daga Covid-19 a Indiya

A yayinda wadanda suka kamu da kwayar cutar Korona a Indiya ya kai miliyan 7.37 ma’aikatar lafiyar kasar ta bayyana cewa yawan wadanda ke warkewa daga cutar ya kai kaso 87.56 cikin dari.

A cikin awanni 24 da suka gabata an bayyan cewa alkaluman kasar sun bayyana cewa an samu karin mutum dubu 63,371 dauke da cutar a jumlace mutum miliyan 7.37 suka kamu da cutar ta Korona.

Haka kuma an bayyana cewa yawan wadanda suka rigamu gidan gaskiya sanadiyar cutara kasar ta Indiya ya kai dubu 112,161.

News Source:   ()