Kawo yanzu Covid-19 ta yi ajalin mutum dubu 292 a doron kasa

Kawo yanzu Covid-19 ta yi ajalin mutum dubu 292 a doron kasa

Kawo yanzu adadin yawan wadanada kwayar cutar Covid-19 ta yi ajali a doron kasa sun kai dubu 292, haka kuma a yayinda mutum miliyan 4 da dubu 342 suka kamu miliyan daya da dubu 602 sun warke.

A kasar Japan mutane 691 sun rasa rayukansu daga cutar inda dubu 16 da 759 suka kamu. A halin yanzu ayawan kasashen da ba'a shiga ba'a fita sun kai 100. Kusan kasashe 13 ne da suka hada da Mexico, Colombia, Uruguay, Honduras, Bahamas, Republic of Kabo Verde, Gabon, Guinea Bissau, Sao Tome and Principe, Equatorial Guinea, Maldives, Azerbaijan da Kazakhstan basa karbar baki daga kasar ta Japan.

Cutar ta Corona ta halaka mutane da dama a kasashe da yawa, ga dai jerin wasu kasashe da yawan wadanda cutar ta yi ajali:

Iran dubu 6 da dari 733, China dubu 4 da dari 633, Indiya dubu 2 da dari 415, Ekwado dubu 2 da dari 327, Russia dubu 2 da dari 116, Pakistan 737, Saudi Arabia 255, Belarus 135, Singapore 21 da Qatar 14.

 

News Source:  www.trt.net.tr