Kusan mutane miliyan 1.2 Corona ta yi ajali a duniya

A duniya baki daya, annobar Corona (Covid-19) ta yi ajalin mutane kusan miliyan 1.2. Adadin wadanda cutar ta kama kuma sun haura miliyan 45.3, yayinda wadanda suka warke kuma suka kusa kaiwa miliyan 33.

A Indiya mutane dubu 121 da 131 ne suka mutu. Mutane miliyan 8 da dubu 88 ne suka kamu da cutar a kasar.

A Iran mutane dubu 34,113 ne suka mutu yayinda adadin wadanda suka kamu ya tashi zuwa dubu 596 da dubu 941.

Adadin wadanda Corona ta kashe a rasha ya tashi zuwa dubu 27,301 sai wadanda suka kamu da suka karu zuwa miliyan da dubu 581.

 

News Source:   ()