Mesut Özil ya bayar da gudunmowar dala dubu 100 domin Ramadana

Mesut Özil ya bayar da gudunmowar dala dubu 100 domin Ramadana

Shahararren dan kwallon kafar English League na kungiyar Arsenal Mesut Özil ya bayar da gudunmowar Lira dubu 713 fiye da dala dubu 100 domin ciyar da magidanta 114 da kuma rabawa mabukata kayan abinci domin wata mai alfarma Ramadana.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Kasar Turkiyya ta fitar da sanarwar cewa  Mesut Özil ya bayar da gudunmowar Lira dubu 713 fiye da dalar Amurka dubu dari domin tallafawa mabukaka a karkashin shirinta na "Taya ni karar da bakin ciki"

Sanannen dan kwallon ya ciyar da mutum dubu 16 bude baki, rabawa dubban iyalai abinci a Turkiyya da Siriya, daukar nauyin bude bakin mutum dubu 90 a Mogadishu; da haka Mesut ya tallafawa mutum 114 a cikin wannan watan mai alfarma.

Mesut Özil a bukin daurin aurensa a shekarar bara ya baiwa hukumar bayar da agajin gaggawa ta Turk Kizilay gudunmowar ciyar da mutum dubu 16.

 

News Source:  www.trt.net.tr