Mummunan hatsarin jirgin sama a Amurka

Mummunan hatsarin jirgin sama a Amurka

Mutane 4 sun rasa rayukansu sakamakon fadowar wani jirgin sama mai saukar ungulu a yankin Colusa da ke jihar California ta Amurka.

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Amurka ta sanar da cewa, jirgin samfurin Robinson R66 ya fado a Colusa da tsakar ranar Litinin din nan.

Shugaban 'yan sandan Calusa ya shaidawa tashar talabijin ta KXTV cewa, mutane 4 da ke cikin jirgin sun mutu nan take. 'Yan sanda yankin ba su bayyana sunayen wadanda suka mutun ba.

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Amurka da Kwamitin Tsaron Sufuri za su gudanar da bincike kan musabbabin hatsarin.

News Source:   ()