Mutum 10 sun hallaka a harin ta'addancin a Siriya

Mutum 10 sun hallaka a harin ta'addancin a Siriya

An sanar da cewa harin ta'addancin da aka kai a Bab da Azez dake arewacin kasar Siriya ya yi sanadiyar rayukan mutum 10 da raunana 24.

Bama-baman dake cikin wata mota ne dai suka tashi a kuda da ma'aikatan al'adun kasar dake garin Azez.

A gurin dai mutum 4 sun rasa rayukansu inda wasu 20 kuma suka raunana.

Jin kadan bayan afkuwar hakan kuma a garin bab mai nisan kilomita 5 daga gabashin Zerzur wani abin fashewa ya tashi daga cikin wata mota.

A lamarin mutum 6 sun rasa rayukansu inda wasu 4 suka raunana.

 

News Source:   ()