Mutum 7 sun rasa rayukansu a rikicin Jammu Kashmir

An sanar da cewa a wata sabuwar rikici da ta barke tsakanin 'yan tawaye da jami'an tsaron Indiya a yankin Jammu Kashmir 'yan tawaye biyu da jami'an tsraon Indiya biyar sun rasa rayukansu.

Dangane ga labaran da kafafaen yada labaran Indiya suka rawaito a yankin Kupwara an kwashi rikici tsakanin 'yan tada zaune tsaye da jami'an tsaro. 

Daga cikin sojojin Indiya da suka rasa rayukansu har da Kanal da Manjo haka kuma 'yan tawaye biyu ma sun rasu.

 

News Source:  www.trt.net.tr