Rahoto: An rusa fiye da Masallatai 8,500 a Xinjiang

Rahoto: An rusa fiye da Masallatai 8,500 a Xinjiang

Wata hukumar bincike ta kasar Ostraliya ta bayyana cewa China ta rushe dubban Masallatai a yankin Xinjiang dake kasar a cikin wani rahotan ta akan yadda ake take hakkokin bin adama a yankin.

Hukumomin kare hakkin bil adama sun bayyana cewa fiye al’umman Uighurs miliyan daya da mafi yawansu Musulmai ai ainihin akabilar Turkawa sun fuskanci ukuba a sansanin dake arewa masu yammacin yankin kasar.

Rahoton Hukumar Bincike ta Kasar Ostariliya ta (ASPI) ta bayyana cewa kimanin Masallatai dubu 16,000 aka rushe ko aka lalata kamar yadda alkalumanta suka nuna.

Rahoton da jaridar Daily Sabah ta rawaito  ya nuna cewa an rusa fiye da Masallatai 8,500 kuma mafi yawan rusau din ya afku ne a cikin shekaru uku da suka gabata musanman a yankin Urumqi da Kashgar.

News Source:   ()