Sakatare Janar na NATO zai ziyarci Turkiyya da Girka

Sakatare Janar na NATO zai ziyarci Turkiyya da Girka

Babban sakataren janar na Kungiyar NATO Jens Stoltenberg zai kawo ziyara Turkiyya a ranar Litini.

Kamar yadda Hukumar ATO ta kasar Tiurkiyya ta sanar sakatare  Stoltenberg zai ziayarci Turkiyya da Girka a makon gobe.

Stoltenberg, a ranar Litini zai kasance a Ankara babban birnin Turkiyya inda zai gana da Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlüt Çavuşoğlu da kuma wasu manyan jami'an gwamnatin kasar.

Stoltenberg wanda kuma zai ziyarci Atina a ranar Talata zai gana da firaiministan Girka  Kiryakos Miçhotakis, ministan harkokin wajen kasar Nikos Dendias da kuma ministan tsaron kasar Nikos Panagiotopulos.

Kungiyar NATO, wacce ta dauki tsawon lokaci tana tattaunawa da Turkiyya da Girka na daukar sabbin salon da zasu haifar da raba iyakokin yankin Gabashin Bahar Rum tsakanin kasashen biyu.

 

News Source:   ()