Saudiyya ta kakkabo jirgi mara matuki mallakar Houthi

Saudiyya ta kakkabo jirgi mara matuki mallakar Houthi

Dakarun da Saudiyya ke goyawa baya sun sanar da kakkabo wani jirgi mara matuki mallakar kungiyra Houthi da Iran ke goyawa baya a Yaman.

Kamar yadda kanfanin dillancin labaran Saudiyya ta (SPA) ta sanar, mai magana da yawun kungiyar hadakar Larabawa Turki el-Maliki, ya sanar da cewa sun yi nasarar kakkabo wani jirgi mara matuki mallakar Houthi a kasar Yaman. Maliki ya kara da cewa an yi yunkurin amfani da jirgin mara matuki ne domin kai hari ga farar hula a Saudiyya.

Kawo yanzu dai kungiyar Houthi ba ta ce komai ba game da lamarin.

A Yaman da ake ci gaba da fama da rikicin siyasa tun daga shekarar 2014 ne kungiyar Houthi da Iran ke goyawa baya keda ikon babban birnin Sana da wasu yankunan yankin.

Kasar Saudiyya kuwa daga watan Maris din shekarar 2015 ta jagoranci tawagar yaki da Houthi a kasar ta Yaman ta hanyar baiwa gwamnatin yaman din gudunmowa.

 

News Source:   ()