Shugaban China ya kare matsayin kasarsa kan yaki da Covid-19

Shugaban China ya kare matsayin kasarsa kan yaki da Covid-19

Shugaban China, Xi Jinping ya kare matsayin kasarsa kan dandamalin kasa da kasa a karo na farko a yayin da ake sukarsu kan barkewar sabon nau'in cutar coronavirus (Covid-19).

Ya yi wannan jawabi ne a yayin Taron Lafiya ta Duniya na 73 wanda aka gudanar kan yanke shawarar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta hanyar wayar tarho.

Da yake mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar barkewar cutar corona a duniya, shugaba Jinping ya ce kasarsa ta sauya hanyar cutar tare da kare rayuwa da lafiyar mutane bisa ga kwazon kokarin da aka yi a kan yaki da barkewar Covid-19.

Ya kara da cewa, 

"Mun gudanar da aiyukan mu da bayyana gaskiya da kuma daukar nauyi tun daga farko har zuwa karshe."

Tare da nuna cewa sun ba da bayanai ga WHO da sauran kasashe a lokacin da annobar ta afku ya ce,

"Mun raba matakan da muka dauka da magungunan mu da duniya ba tare da bata lokaci ba. Mun yi duk abin da za mu iya don tallafawa da kuma taimakon kasashen da ke cikin bukata." 

An soki gwamnatin Beijing saboda kokarin rufe barkewar cutar a kwanakin da ta fara bayyana, ba tare da gargadi ga WHO da sauran kasashe kan lokaci ba.

News Source:  www.trt.net.tr