Sojojin Isra'ila sun kashe wani yaro Bafalasdine

Sojojin Isra'ila sun kashe wani yaro Bafalasdine

Sojojin Isra'ila sun kai farmaki a garin Al-Halil na Yammacin Gabar Kogin Jordan da Yahudawa suka mamaye inda suka kashe wani yaro Bafalasdine inda suka jikkata wasu Falasdinawan 4.

Rubutacciyar sanarwar da Ma'aikatar Lafiya ta Falasdin ta fitar ta cesojojin na Isra'ila sun harbi wani yaro dan shekaru 15 mai suna Zaid Fazi Kasiyye a sansanin 'yan gudun hijira na Fawwar da ke garin Al-Halil a kansa.

Sanarwar ta ce sakamakon rikicin da ya barke a sansanin an kuma jikkata wasu Falasdinawan 4 bayan harbin su da harsashan gaske wadanda an kai su zuwa asibiti don samun kulawa.

Shaidun gani da ido sun cesakamakon kai farmaki da sojojin Isra'ila suka yi a sansanin Al-Fawwar ne ya janyo Falasdinawa yin bore.

Sojojin Isra'ila sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye, harsashan roba da na gaske don tarwatsa masu Falasdinawan. An bayyana samun mummunar arangama a tsakaninsu.

Sojojin Isra'ila na yawan kai sumame a Yammacin Gabar Kogin Jorda da Gabashin Kudus da Yahudawa suka mamaye inda suke kama Falasdinawa bisa zarge-zarge daban-daban.

 

News Source:  www.trt.net.tr