Sojojin lsra'ila sun tsare Falasdinawa 11

Sojojin lsra'ila sun tsare Falasdinawa 11

Sojojin Isra’ila sun tsare Falasdinawa 11 a Yammacin Kogin Jordan da suka mamaye, ciki har da Nadir Safafta, daya daga cikin shugabannin Hamas a yankin.

A cewar bayanan da aka samu daga majiyoyin yankin, an bayyana cewa wata runduna ta musamman da ke da alaka da sojojin Isra’ila ta kai samame a garin Tubas da ke Yammacin Gabar Kogin Jordan tare da tsare Safafta, daya daga cikin shugabannin yankin na Hamas.

Har yanzu Hamas da sojojin Isra’ila ba su yi wani bayani ba game da tsare Safafta.

Haka kuma Sojojin Isra’ila sun tsare Falasdinawa 10 daga garuruwan Yammacin Kogin Ramallah da Nablus.

News Source:   ()