Tarayyar Turai da China sun amince kan yarjejeniyar saka hannun jari

Tarayyar Turai da China sun amince kan yarjejeniyar saka hannun jari

An cimma yarjejeniyar saka hannun jari a tattaunawar tsakanin Tarayyar Turai (EU) da China da aka fara tun shekarar 2014.

Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen, Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Charles Michel, Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel, Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Shugaban China Xi Jinping sun gudanar da "Taron Shugabannin EU da China" ta hanyar sadarwa ta bidiyo.

A wata sanarwa da kungiyar EU ta fitar a karshen taron, an bayyana cewar da zarar yarjejeniyar ta fara aiki, za ta taimaka wajen daidaita dangantakar kasuwanci da saka hannun jari tsakanin EU da China.

Sanarwar ta yi nuni da cewa kasar China ta amince da ba masu saka hannun jari na EU damar shiga kasuwarta a matakin da ba a taba gani ba. An kuma bayyana cewar yarjejeniyar ta sanya a fili wajibai kan kamfanonin gwamnati na kasar China, da hana yin amfani da fasahar tilas da sauran aiyukan rudani a kasuwanni da kuma sa goyon bayan jama'a ya zama a bayyane.

Sanarwar ta kara da cewa za a yiwa kamfanonin Tarayyar Turai adalci yayin da suke gasa a kasuwar kasar China.

 

 

News Source:   ()