TIKA ta taimakawa gidan marayun Afghanistan da kayayyaki

TIKA ta taimakawa gidan marayun Afghanistan da kayayyaki

Hukumar Hadin Kai da Kulawa ta Turkiyya (TIKA), ta taimakawa gidan marayun dake lardin Sar-i Pul a arewacin kasar Afghanistan da kayayakin amfanin yau da kullum.

Kamar yadda bayanai suka fito daga ofishin TIKA dake Mezar-ı Şerif, an taimakawa yara 60 dake gidan marayun  garin Sar-i Pul da gadaje, barguna, sutura da makamantansu.

TIKA wacce ta farantawa dukkanin yaran dake gidan marayun Sar-i Pul rai, ta bayyana cewa ya kamata gidan marayun ya zama irin na zamani ta yarda zai kasance da dukkanin komai da yaran ke bukata.

 

News Source:   ()