Titunan garin Portland na Amurka sun zama filin yaki

Titunan garin Portland na Amurka sun zama filin yaki

Wutar rikici ta sake ruruwa a garin Portland na Amurka tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar adawa da amfani da karfin da ya wuce ka'ida da jami'an tsaron kasar ke yi.

Gwamnar jihar Oregon Kate Brown ta bayyana cewar jami'an tsaro na tarayya da suka je Portland bayan an bude wuta kan ginin kotun tarayya za su fara janyewa daga yankin.

Amma masu zanga-zangar sun sake fita kan tituna tare da yin arangama da 'yan sanda. 'Yan sandan tarayya sun harba wa masu zanga-zangar hayakimai sa hawaye.

A garin Portland ne ake gudanar da zanga-zanga ta tsawon makonni tun bayan kisan bakar fata George Floyd da 'yan sandan Amurka suka yi.

News Source:   ()