Turkiyya ce kasa ta 8 dake da yawan wadanda aka yiwa alluran riga-kafin Korona

Turkiyya ce kasa ta 8 dake da yawan wadanda aka yiwa alluran riga-kafin Korona

Turkiyya ce kasa ta 8 da aka fi samun yawan wadanda aka yiwa alluran rigakafin Korona a doron kasa.

Kawo yanzu a fadin duniya an yiwa mutum fiye da biliyan 1 da miliyan 370 allurar rigakafin (Covid-19).

Turkiyya ta kasance ta 8 a duniya inda aka yiwa mutum miliyan 25 da dubu 476 dubu 915 allurar rigakafin Koronar.

Mutane miliyan 14 da dubu 767 dubu 72 ne suka karbi kason farko sannan mutane miliyan 10 da dubu 709 dubu 843 suka karbi kashi na biyun allurar.

A cewar shafin "Ourworldindata.org", inda aka tattara bayanan rigakafin Kovid-19, China ce kasar da ta fi yawan wadanda aka yiwa alluran rigakafi a duniya tare da allurai miliyan 354 miliyan 272, sai Amurka da miliyan 264 miliyan 680, Indiya da miliyan 176 da dubu 45, sai Birtaniya da miliyan 54 da dubu 160, Brazil da miliyan 49 da dubu 188, Jamus da miliyan 36 da dubu 837, Faransa da miliyan 26 da dubu 806, Turkiyya da miliyan 25 da dubu 466 da dari 743, sai Italiya da miliyan 25 da dubu 404, Rasha da miliyan 22 da dubu 575 , Indonesiya da miliyan 22 da dubu 536, sai Mexico da miliyan 21 da dubu 300 sai kuma Spain na bin su baya da miliyan 20 da dubu 623.

News Source:   ()