Turkiyya ta bayyana damuwarta akan kame Celal mataimakin shugaban majalisar Tatar

Turkiyya ta bayyana damuwarta akan kame Celal mataimakin shugaban majalisar Tatar

Turkiyya ta bayyana cewa ta damu da yadda jami’an tsaron Rasha ke tsare da Neriman Celal, Mataimakin Shugaban Majalissar Tatar (KTMM) a yankin Crimea da Rasha ta kwace ba bisa ka’ida ba.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya, Tanju Bilgic, ya ba da amsa a rubuce ga tambayar game da tsare mataimakin shugaban farko na majalisar Tatar Crimea Neriman Celal.

Da yake bayyana cewa sun samu labarin cewa an kama Celal bayan samamen da aka kai gidansa da ke Crimea a safiyar jiya, an kai shi wani wuri da ba a sani ba kuma har yanzu ba a ji duriyarsa ba.
Ya kuma kara da cewa,
"Muna bin abubuwan da ke faruwa cikin aihini, kuma muna fatan Neriman Celal da 'yan Tatar hudu na Crimean da aka kama tare da shi za su koma gidajensu da danginsu da wuri -wuri." 

News Source:   ()