Turkiyya ta kyamaci harin da aka kai Pakistan

Turkiyya ta kyamaci harin da aka kai Pakistan

Ķasar Turkiyya ta yi tir da Allah wadai da harin da aka kai a Arewacin Waziristan dake jihar Belujistan a kasar Pakistan. 

Ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ce ta fitar da sanarwa a rubuce inda take bayyana bakin cikin samun labarin harin da aka kai a jihar Belujistan a kasar Pakistan da ya yi sanadiyar rasa rayukan jami'an tsaro da dama.
Sanarwar ta kara da cewa "Wannan bakin harin ta'addanci, muna masu nuna kyama da yin Allah wadai da shi, muna kuma yin adduar samun rahamar Ubangiji ga wadanda suka rigamu gidan gaskiya da kuma fatar samun sauki cikin gaggawa ga dukkanin alumman da suka raunana "
A harin da aka kaiwa tawagar jami'an tsaro a jihar Belujistan a kasar Pakistan hadi da sojoji 11 mutum 14 sun rasa rayukansu; haka kuma a Arewacin Waziristan an kai harin bam da ya yi sanadiyar rasa rayukan jami'an tsaro shida.

 

News Source:   ()