Wadanda zayzayar kasa ta kashe a Indonesiya sun haura 18

Wadanda zayzayar kasa ta kashe a Indonesiya sun haura 18

A kasar Indonesiya yawan wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar zayzayar kasar da tsananin ruwan saman da aka yi a ranar 14 ga watan Febrairu ya haura 18.

A kauyen Ngetos da aka samun afkuwar zayzayar kasar masu aikin ceto da bincike sun yi nasarar gano wasu jikkunan mutum 6.

Hukumomin sun bayyyana cewa yawan wadanda suka rasa rayukansu ya haura 18. Kawo yanzu dai ana cigaba da neman wani mutum daya.

Zayzayar kasar da ta daushe mutum 21 an yi nasarar tono biyu raye.

 

News Source:   ()