Wani dan majalisar Afghanistan ya tsallake rijiya da baya

Wani dan majalisar Afghanistan ya tsallake rijiya da baya

An sanar da cewa mutum biyu suka rasa rayukansu a yayinda wasu biyu kuma suka raunana a wani harii da aka kai kasar Afghanistan.

Lamarin dai ya faru a yankin Hayirhane inda wani bama da aka ajiye akan motar sojoji ya tashi.

Dangane ga bayanan da aka samu daga shaidun gani da ido an yi niyyar kai harin ga motar wani dan majalisa.

Kawo yanzu dai ba a dora alhakin kai harin akan kowa ba.

News Source:   ()