Yahudawa sun bankawa gonar zaitun din Falasdinawa wuta a Gaza

Yahudawa sun bankawa gonar zaitun din Falasdinawa wuta a Gaza

Yahudawa 'yan tada zaune tsaye sun bankawa gonakin itacen Zaitun mallakar Falasdinawa wuta a yankin Zirrin Gaza.

Kamar yadda kanfanin dillacin labaran Falasdin ta WAFA ta rawaito, wasu Yahudawa 'yan tada zaune tsaye sun bankawa wata gonar zaitun wuta dake yankin Al Halil a karkashin gundumar Mesafir Yatta.

Sanarawar ta kara da cewa Yahudawan sun jefa bam din kwalba ne a cikn gonar zaitun din Falasdinawa lamarin da ya haifar da kamawa da wuta da ya yi sanadiyar konewar bishiyoyin zaitun fiye da 400.

An sanar da cewa Yahudawan da suka sanya wutar sun fito ne dag matsugunan Yahudawan Mitzpe Yair, kuma an yi nasarar hana wutar yaduwa zuwa gidajen da ke yankin sakamakon kokarin da hukumar kashe gobara ta Falasdinu ta yi wajen kashe wutar.

 

News Source:   ()