'Yan ta'addan DEASH sun hakawa sojojin Iraki tarko

'Yan ta'addan DEASH sun hakawa sojojin Iraki tarko

An sanar da cewa tashin tarkon bam din da 'yan ta'addan DEASH suka haka ya yi sanadiyar rayuwan soja daya da raunanan biyu a Kerkuk dake kasar Iraki.

Rundunar sojan Iraki ce ta sanar da cewa ta kai farmakin kauda 'yan ta'addan DEASH a yankin garin Diblis dake karkashin gundumar Kerkuk.

A farmakin a yayinda sojojin suka shiga cikin wani kogon da 'ayna ta'addan ke boyewa bam din da suak haka a matsayin tarko ya tashi.

Shugaban 'yan sandan Kerkuk Ali Kemal ya bayyana cewa an tayar da bam din ne daga nesa ta amfani da remote.

An dai kara kaimin farmakin da ake kaiwa yankin.

News Source:   ()